Wata ƙungiya mai suna: Ƙungiyar wayar da kai domin zaƙulo Shuwagabanni na gari, a Jihar Katsina, tayi tattaki a gidan Sanata Sadiq Yar’Adua domin miƙa mubaya’arsu da nuna goyan baya ga Sanatan don tsayawa Takarar Gwamnan jihar Katsina.

Da yake jawabi a madadin Shuwagabannin ƙungiyar na yankuna (Zones) Shugaban Kungiyar Alhaji Tijjani Sani Kofar Guga ya gabatar da Ayyukan kungiyar a gaban Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua, inda ya zayyani kadan daga cikin Ayyukan kungiyar Kamar haka “Kungiyar mu ta samar ma Matasa Aikin yi, tana Tallafawa Marayu, ta ginama wata Baiwar Allah gidan zama a lokacin da gidanta ya rushe kuma bata da karfin ginawa, muna hada kuɗaɗe domin taimakawa Al’uma ta janibobi daban daban kuma muna yi ba don Siyasa ba. Mai girma Sanata Babban Aikin da Muka sanya a gaba, shine wayar da kan Al’uma da nuna masu Cancantar zaɓen Mutumin kirki a shugabanci, kuma ko wace jam’iyyar ya fito domin ciyar da jihar mu gaba, Don hakama a cikin mu akwai dan ‘yan PDP da ‘yan APC da sauran Jam’iyyu”

Da yake tsokaci, a wajen Sanata Yar’Adua yace: “Abinda nake ƙara nanatawa ga Al’uma shine, na fito takara ne domin ganin halin da Al’uma ta shiga, kuma ina ganin akwai gudumawar da zan iya bada wa domin cika Umarnin Allah, cewa Idan kaga Ana barna ka yaketa da Dukiya, Ilimi, Karfi, Ko kuma ka kyamaci abin. To Alhamdulillah duka zanyi iya iyawata domin in sauke haƙƙi, kuma ina kira gareku da kufito a yi yaƙin nan daku, domin ko anje lahiri kuna da Hujja a gaban Allah.”

Taron da ya gudana a Ranar Asabar 1/1/2022 ya samu halartar duka shuwagabannin yankunan Daura, Funtua da Katsina, da kuma shugabar Mata ta ƙungiyar Membobi da sauran Al’uma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here