Home City News Yar Najeriya ta lashe kujerar Majalisar Wakilan Amurka

Yar Najeriya ta lashe kujerar Majalisar Wakilan Amurka

Yar Najeriya ta lashe kujerar Majalisar Wakilan Amurka

..

Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a Amurka, Esther Agbaje, ta lashe kujerar Majalisar Wakilai ta Amurka, a zaɓen ƙasar na 2020.

Jaridar The Punch a Najeriya ta ruwaito cewa Agbaje ta kayar da abokin hamayyarta, Alan Shilepsky a zaɓen.

Ta samu kuri’u 17,396, wanda hakan ke nufin ta samu kashi 74.6 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Shilepsky na Jam’iyyar Republican ya samu ƙuri’u 4,128, wanda hakan ke nufin ya samu kashi 17.7 cikin 100 na ƙuri’un da aka jefa.

Ms Agbaje wacce ta karanci ilimin shari’a a Jami’ar Harvard da kuma digiri na biyu a Jami’ar Pennsylvania, ta yi aiki a ofishin harakokin wajen Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: