Yanzu-yanzu: Bamalli ne Sarkin Zazzau na 19 – Kotu ta yanke hukunci.

Babbar kotun jihar Kaduna dake zaune a Dogarawa, Sabon Garin Zariya yanzu nan ta yanke hukunci cewa Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ne sahihin Sarkin Zazzau na 19. Daily Trust ta ce Alkali Kabir Dabo, wanda ya yanke hukuncin ya ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i zai iya nada sarkin ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, 2020. Wannan hukunci ya biyo bayan karar da Iyaz Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya shigar kan zaben sabon sarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here