Nnamdi Kanu: Yansanda sun saki Sowore, da wasu da aka kama a Abuja

Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Mawallafin Jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore, da wasu da aka kama a lokacin Zanga-zangar da sukayi a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, an sake su.

Sun dai Yi Zanga-zanga ne a matsayin wata girmamawa ga Shugaban Kungiyar Rajin Kafa Kasar Biafra Nnamdi Kanu, Wanda ake Shari’ar shi a halin yanzu.

Awanni Kadan bayan an kama shi, Mai fafutukar cewa Buhari sai ya tafi wato-‘Buhari-Must-Go’, ya sanar dacewa an sake shi da wasu mutane.

Yace “yanzun nan suka sake mu. Sun buge mu, sunci mutuncin mu. Sun kaimu Sakatariyar Yansanda. Na gaya masu basuda damar kama ni.

“Inada damar da zan halarci Shari’ar Nnamdi Kanu. Sun dauki katikan mu, sun goge duk abunda muka nada a waya.”

Dasuke maida martani akan, Kungiyar Gamayyar Fararen Hula tayi Allah wadai da kama Sowore da sauran magoya bayan Shugaban IPOB Nnamdi Kanu.

Jami’in Kungiyar Dimeji Macaulay ya godema Yan Najeriya da suka matsawa Yansanda, suka sako Sowore da sauran wadanda aka kama.

“Muna bukatar Hukumar DSS ta fito ta bamu hakuri a bainar Jama’a akan kamani da Sowore, da wasu yan jarida, gami da yan IPOB, tare da daukar mataki tsatstsaura ga Yansanda da suka kama mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here