Yanzu yanzu: Shugaban hukumar gidajen yari, Ja’afaru Ahmed ya yi murabus

Bayan samun karin wa’adin mulki har sau biyu, daga karshe shugaban hukumar kula da gidajen yarin Najeriya, Ja’afaru Ahmed zai yi murabus daga ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu.

Ahmed dan shekara 61 ya dare mukamin ne a shekarar 2016, kuma wa’adinsa yak are tun a watan Yulin 2019, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarce shi ya cigaba da aiki, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Sharpreporters.com ta ruwaito ma’aikatar cikin gida ta bayyana cewa ta nemi shugaban kasa ya kara masa wa’adi ne duba da kyawawan aikin da ya gudanar a hukumar don ba shi daman kammala ayyukan da ya faro.

Haka zalika bayan karewar karin shekara guda da shugaban kasa ya kara masa a watan Yulin 2020, Ahmed bai sauka ba, inda aka sake kara masa wani shekara dayan.

Sharp Reporters

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here