Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi murabus da ga jam’iyar PDP.

Kwankwaso ya baiyana ficewar sa da ga jam’iyar PDP ne a wata wasiƙa da ya rubuta ya kuma aike wa Shugaban jam’iyar na mazaɓar sa a yau Talata.

A wasiƙar, Kwankwaso, tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ya ce “ga dukkan girmama wa, ina mai rubuta naka wannan wasiƙa domin na shida maka cewa, sakamakon rikici mai zafi, wanda babu alamun sasanta wa, shine ya sanya na ke ganin ci gaba da zama na a jam’iyar PDP ba zai yi wu ba.

“Shi ne, da ga yau Talata, 29 ga watan Maris, 2022, na yi murabus da ga zama ɗan jam’iyar PDP,” a cewar wasiƙar.

Wannan matakin na Kwankwaso ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da a ka dade a na yi na cewa zai fice da ga jam’iyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here