Babbar kotun shari’ar musulunci dake kofar kudu a birnin jihar Kano ta dage zaman sauraren shari’ar Sheakh Abduljabbar Kabara da ake tuhuma da sakin wasu maganganun batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bayyana cewar, bayan kotun ta fara zaman farko kan lamarin kuma ta soma sauraren bayanai daga kowane bangaren lauyoyi to ta dage zaman shari’ar daga yau laraba zuwa ranar 18 ga watan Augusta na wannan shekarar 2021.

Alkali Ibrahim Sarki Yola ya bayar da umurnin cigaba da tsare Abduljabbar Kabara a gidan kaso har lokacin da kotun zata cigaba da zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here