Advert
Home Sashen Hausa Yanzu-Yanzu: Garba Shehu da Lai Mohammed, sun kamu da cutar Koroma

Yanzu-Yanzu: Garba Shehu da Lai Mohammed, sun kamu da cutar Koroma

Yanzu-Yanzu: Garba Shehu da Lai Mohammed, sun kamu da cutar Koroma

Sabuwar nauyin cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami’an gwamnati suka kamu da cutar. Premium Times ta bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar.

Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Hakazalika akwai Ministan Labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shima sakamako ya nuna Korona ta hau shi.

Rahoton ya kara da cewa a ranar Laraba, an yakice Garba Shehu da wasu daga taron majalisar zartaswa ranar Laraba yayinda sakamakon gwajin PCR ya fito.

Garba Shehu ya tabbatar da cewa lallai ya kamu da cutar a sakon da Premium Times tace ta gani.

Yace: “Ban da tabbacin wadannan mutanen da ka ambata amma na kamu da sabon nauyin cutar maras tsanani.

Tun farko ban ji komai ba, la’alla saboda na yi rigakafi sau uku ne, amma yanzu garau nake ji.” “Amma matsalar cutar nan itace sai abinda masana kimiya suka fada cewa kaji sauki.

Yanzu dai ina killace kuma zan koma in sake gwaji don ganin ko har yanzu akwai cutar ko ta tafi.”

Duk yunkurin yi daga bakin Lai Mohammed, Femi Adesina, Tolu Ogunlesi, ya ci tura.

Amma majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa dukkan jami’an da suka kamu na killace kuma ana kula da su.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Jam’iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa

Jam'iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa Babbar jam'iyyar adawa a jihar...

Aisha Buhari Ta Naɗa Kashim Shettima A Matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu Na Kwalejin Future Assured

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta naɗa Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na Kwalejin Future Assured da ke...

WHICH PARTS OF NIGERIA ATTRACTED MORE FOREIGN INVESTMENTS IN THE YEAR 2021?

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/262020019347856/

AGAIN, A NEW ADDITION TO NIGERIA’S MARITIME SECURITY VESSELS!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/261866049363253/

Jami’an Hukumar yaƙi da yima Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annuti ta ICPC sunyi Dirar Mikiya jihar Katsina….

Jami'an Hukumar sun gano yadda akayi Haɗin baki da Ɗan Majalisar Wakilai da kuma Mai duba ƙwangila aka sace kuɗin ƙwangilar Naira Milyan Talatin...