Darakta-Janar na Inuwar Gwamnonin APC, Salihu Lukman ya ajiye muƙamin sa.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ajiye muƙamin na sa na da nasaba da rikicin jam’iyar da ya dabaibaye batun babban taron jam’iyyar na ƙasa.

Vanguard ta jiyo cewa ajiye muƙamin na Lukman ya faru ne lokacin da Inuwar Gwamnonin APC ɗin ke ganawa ta sirri a jiya Lahadi da daddare, in da su ka ce ya fiye surutu.

Amma kuma wasu gwamnoni da dama da ke wajen ganawar ba su goyi bayan ajiye aikin nasa ba duba da cewa ya na magana ne a matsayin sa na Darakta-Janar kuma ƙasa a jam’iyar.

Duk da cewa Lukman bai yi magana da manema labarai ba, wata majiya ta ce ya yi daidai tunda ya ɗauki mataki ne da ya ke ganin ya yi daidai a tunanin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here