Kungiyar malaman jami’o’i ta dage matakin da ta dauka na yajin aikin, inda ta ce ana ci gaba da tuntubar juna.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taron ta na majalisar zartarwa ta kasa.

Tun da farko ASUU ta bayyana shirin shiga yajin aikin saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun ta.

“Duk da haka, la’akari da kokarin shiga tsakani da tuntubar da ake yi, NEC ta yanke shawarar sake duba lamarin nan gaba da nufin yanke hukunci kan mataki na gaba.”

Daily trust hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here