Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu

Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari

An kama Omoyele Sowore, mai gidan jaridar Sahara Reporters a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yayin da kotu ta ke ci gaba da shari’ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun cafke dan gwagwarmayar ‘Buhari-Must-Go’ a harabar kotun yayin da yake daukar bidiyon kai tsaye na Facebook da safiyar Litinin, Punch ta ruwaito.

A baya an bayar da rahoton cewa an sanya tsauraran matakan tsaro a kusa da kotun yayin da ake ci gaba da shari’ar Kanu, wanda ya kasance a hannun jami’an DSS a yau.

Kanu, wanda tun farko aka dawo da shi Najeriya daga wata kasar waje, yana fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da ta’addanci a gaban Mai shari’a Binta Nyako.

‘Yan jarida a kofar kotun, jami’an DSS sun hana su shiga kotun a kan cewa ba a ba su izinin ba su rahoton shari’ar ba.

An kuma ruwaito cewa ‘yan sanda na sirri sun hana wasu kungiyoyin ‘yan jarida daukar rahoto kan shari’ar shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, yayin da ake ci gaba da shari’arsa a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here