Advert
Home Sashen Hausa Yanzu-Yanzu: An rufe kwallejin Ilimi Ta Tarayya Dake Jihar Adamawa

Yanzu-Yanzu: An rufe kwallejin Ilimi Ta Tarayya Dake Jihar Adamawa

Daga Muhammad Kwairi Waziri

An rufe kwallejin ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE, da ke Yola a jihar Adamawa saboda zanga-zangar da dalibai suka gudanar a yau talata.

Sun yi zanga-zangar ne saboda nuna rashin ruwa da wutar lantarki na wasu kwanaki a makarantar.

Hukumar Makarantar ta bayyana cewa sun bada umarnin fara gyaran ruwan amma duk da haka daliban ba su dena zanga-zangar ba hakan yasa aka rufe makarantar.

Zanga-zangar dalibai dai ya janyo rikici Kuma ya jawo rufe kwallejin ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE, da ke Yola a jihar Adamawa.

Sai dai dalibai sun fusata sunyi yunkurin lillalisa malaman su, sai dai zuwa yanzu sun jikkata wasu daga cikin malaman su.

Zuwan jami’an tsaron ya fusata daliban wadda hakan yasa suka fara cinnawa gine-gine wuta tare da fasa shaguna a makarantar.

Wani dalibi, wanda ya ce a sakaya sunansa ya bayyana cewa sun shafe kwanaki a kwalejin babu ruwa babu wuta.

Ya kara da cewa: “An bar mu muna rayuwa a mawuyacin hali, Ka dubadalibai fiye da 5000 a makarantar nan muka shafe kwanaki babu ruwa, sai mun fita cikin gari neman ruwa, Sannan muna da matsala da wutar lankarki.”

Mahukunta makarantar sun amsa cewa ruwan makarantar ya samu matsala amma sun musanta cewa an bar daliban tsawon kwanaki babu ruwa.

Rajistarar kwallejin, Ahmad Gidado ya ce bututun ruwan da ke kawo ruwa makarantar ne ya lalace.

Rajistaran Makarantar ya kara da cewa sun dukufa sun fara aiki nan take bayan samun rahoton matsalar ruwan a jiya (Litinin), an umurci sashin ayyuka na makarantar ta gyara ruwan, amma aka farko ranar Talata aka ga dalibai na zanga-zanga.

Gidado ya ce kwallejin na da wasu rijiyoyin burtsatse amma saboda dalibai fiye da 5000, suna amfani da tankin ruwa domin kawo ruwa makarantar saboda lalacewar bututun ruwan.

“A safiyar yau tankin ruwa tana raba wa dalibai ruwa a wuraren diban ruwa amma ba su dena zanga-zangar ba. Domin kada abubuwa su tabarbare, an yi taron gagg

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yansanda A Katsina Sun Chika Hannu Da Yan Kungiyar Asiri Biyu

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne. Kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na...

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...