Yanzu-Yanzu Abdulsalam Abubakar ya mayar da martani kan zargin da ake masa na ta’adda

Jama’a kar ku yarda da labarin da ake yadawa cewa an kama jirgin sama mai kai wa ‘yan bindiga abinci da makamai mallaki na~ Abdulsalam Abubakar

Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya karyata labarin da ake yawo da shi cewa an cafke wani jirgin sama mai saukar ungulu wanda ake zargin yana kai wa ‘yan bindiga kayan abinci da kuma yaki a jihar Neja.

Abulsalam ya bayyana cewa wannan labari ba gaskiya bane, sannan kada kowa ya yarda da wannan labari. Domin labari ne wanda aka kirkira don a bata masa suna.

Tun jiya dai ne ake ci gaba da yada wannan labari wanda aka alakanta Abdulsalam da shi.

Daga karshe tsohon shugaban kasar ya roki Allah ya kawo wa ma Najeriya zaman mai dorewa.

Daga: Dr Yakubu Sulaiman Media Aid to Abdulsalan Abubakar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here