Shahararren ɓera da aka bai wa lambar yabo ta zinare – saboda ya gano nakiya da dama – ya rasu yana da shekara takwas a duniya.

A shekara biyar da ya shafe ta aikinsa, Magawa ya gano nakiya (bam da ake binnewa a ƙasa) fiye da 100 da sauran abubuwan fashewa a Cambodia.

Magawa ne ɓera mafi nasarori a duniya da ya samu horo daga cibiyar Apopo ta ƙasar Belgium domin ya dinga ankarar da mutane inda aka binne nakiya saboda a bankaɗo su.

Cibiyar ta ce ɓeran ɗan asalin Afirka ya “rasu ba tare da rashin lafiya ba” a ƙarshen mako.

Ta ƙara da cewa Magawa na cike da ƙoshin lafiya “har ma ya shafe mafi yawan makon da ya gabata yana wasa cikin annashuwa kamar yadda ya saba”.

Amma ya zuwa ƙarshen mako “sai ya fara sassautawa tare da yin barci da yawa da kuma ƙin cin abinci a ranakunsa na ƙarshe”.

Source: BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here