Daga Hausa Daily Times -June 17, 2021

Rahotanni dake fitowa daga ƙaramar hukumar Yauri na jihar Kebbi na cewa ƴan bindiga masu garkuwa da mutane sun shiga Makarantar Sakandaren maza ta Gwamnatin Tarayyaa (FGC) dake Birnin Yauri.

Wani mazauni garin da ya nemi a saƙaya sunansa ya shaidawa Hausa Daily Times cewa maharan dama sun bada sanarwa za su shiga Yauri a wani naɗaɗɗen murya da wani matashi ya yi hira da su ta wayan tarho a kwanakin baya.

Da yake tabbatar da kai harin, ya ce sun kashe wani jami’in tsaro tare da tafiya da ɗalibai da malamai da ba a san adadin su ba a cikin motar jami’an tsaro dake gadin makarantar.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundinar ƴan sanda na jihar Kebbi ASP Nafi’u Abubakar amma abin ya ci tura domin duƙiran da wakilin mu ya yi ma layinsa ba a samu ɗaga wa ba kuma ha izuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wani abin da aka ji daga rundinar ƴan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here