Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne.

Kamar yadda Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar SP.Gambo Isah ya bayyana,an chafke wadanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Dutsinma.

S.P Gambo Isah yace daya daga cikin wadanda ake zargin dan Asalin Jihar Kwara ne kuma yana daya daga cikin yan Kungiyar Asiri da Yansanda suke nema ruwa a Jallo.

Dayan wanda ake zargin yace shi dalibin Jami’ar Dutsinma ne kuma yana karantar Nazarin Huldatayya Tsakanin Kasashe wato International Relations.

Kakakin Rundunar Yansandan yace da zarar an kammala bincike za’a mika wadanda ake zargin a gaban Kotu domin fuskantar Hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here