YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA

Da misalin karfe 10:20 na safiyar yau Litinin, Alkalai uku sun shigo a karkashin jagorancin Mai shari’a Musa Danladi Abubakar wanda shi ne Babban Jojin Jihar Katsina.

Sauran alkalan sune Maishari’a Abbas Bawale da Maishari’a Ashiru Sani.

Mustapha Inuwa da Lauyan sa AS Ibrahim sun samu hallara a kotu a yayin da shi kuma Lauyan Mahadi ya shigo ba tare da wanda ya ke tsaya ma wa ba, wata ƙil ko dan ya na wata shari’ar a cikin Birnin katsina.

An kira masu kara inda lauyoyin bangarorin biyu suka mike suka yi bayanin dalilin da ya sanya aka dawo da shari’ar su nan Dutsinma.

Inda lauyan Mustapha Inuwa, Barrister AS Ibrahim ya yi bayanin cewa, ya yi gyaran da aka ba shi damar ya je ya yi dangane da kwanan wata, saboda haka ya roki Kotun ta karbi sabuwar takardar, ta kuma janye waccan tsohuwar, kotun ta tambayi Lauyan Mahadi, ko ya amince da hakan, inda ya ce ya yarda don haka Kotun ta amshi rokon Lauyan Mustapha Inuwa.

Daga nan sai aka bukaci Lauyan Mahadi Shehu Barrister Abbas Abdullahi Machika ya gabatar da koken sa.

Lauyan ya ce; Sun daukaka kara ne suna kalubalantar ingancin sammacin da Kotun Shari’a ta baiwa Mahadi a Abuja, don haka suke neman Kotun da ta dagatar da Kotun shari’ar Musulunci, daga ci gaba da sauraren karar da Mustapha Inuwa ya kai Mahadin a gaban ta.

Kotun tace kowa ya bada bayanen hujjojin sa a rubuce domin yin nazari da fidda matsaya.

Lauyoyin biyu sun amince da wannan shawara don haka Shugaban zaman, Maishari’a Musa Danladi Abubakar ya dage shari’ar zuwa wata rana da za a sanar a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here