Home Sashen Hausa YANDA WATA MATA TA YIWA ƳAƳANTA YANKAN RAGO

YANDA WATA MATA TA YIWA ƳAƳANTA YANKAN RAGO

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu da ake zargin mahaifiyarsu ta yi musu yankan rago.

‘Yan sandan sun ce ana zargin cewa matar ta sami sabani da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watanin baya.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya da ke kwaryar birnin Kanon.

Yaran da ake zargin mahaifiyar tasu ta yanka su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru biyar da yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekaru uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne a jiya Asabar.

Lamarin ya daurewa mutane da dama a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano kai, musamman ga makotan gidan da lamarin ya faru inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar bata da tabin hankali haka kuma ba a santa da shaye-shaye ba.

Amma sai dai wasu, sun kuma alakanta abin da matar ta yi da kishiyar da mjin ta ya yi mata a ‘yan kwanakin baya, wanda har ta kai ga sun samu rashin jituwar da ya janyo mutuwar aure, amma daga baya aka dai-dai ta ta koma dakinta.

Ana neman matar

BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma’ana mijin matar da ake zargi da kashe ‘ya’yan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhali ni da ya ke ciki sakamakon abin da ya faru.

Wani lamarin da yake kara daure kai a cikin batun shi ne rashin sanin inda matar take da kuma halin da take ciki, domin a cewar kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa abin da suka sa gaba yanzu shi ne neman inda matar take, domin tuni suka kaddamar da bincike.

Tuni dai aka yi wa yaran jana’iza a dai-dai lokacin da ake ci gaba da neman mahaifiyarsu da ake zargin ita ta raba su da duniya, bayan ta sha wahalar daukar cikinsu da rainonsu har suka fara zama mutane.

Lamarin dai ya dauki hankulan jama’a da dama musamman ganin irin shakuwar da ke tsakanin da da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi ba zai sa uwa ta hallaka ‘ya’yanta ba, don haka mutane ke fatan samun takamemen amsa duk lokacin da aka samu matar da ake zargi aka kuma gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DOGARO DA KAI; wani matashi mai kwalin Digiri da sana’ar Bola a katsina

  Rahotan wani matashi a jihar Katsina da ya kama sana'ar kwankwani ko kuma jari bola Wanda ya yi karatun NCE kuma ya yi Degree...

“Mu Ne Matsalar Kasarmu” – Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Bauchi.

"Mu Ne Matsalar Kasarmu" - Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Bauchi. "...Malam ka dubi yadda kasarmu ta lalace. Idan wani abu ya faru, sai a...

Komutuwa nayi Idan ana dawowa zan roki Allah ya maidoni a matsayin Danfulani

Ko mutuwa nayi Zan roki Allah ya dawo Dani amatsayin dan fulani, mu fulani ba ‘yan ta’adda bane ~Inji Sarkin musilmi Sultan. Mai Alfarma Sarkin...

Ƙungiyar Arewa ta juyama Gumi baya

Yan bindiga: Ƙungiyar Arewa ta juyawa Gumi baya, ta ce ya je ya ƙwaci kansa Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari Kungiyar dattawan arewa ta nesanta kanta...

Sakamakon zaɓe; Nijar ta turniƙe

Yadda hukumomi a Yamai Jamhuriyar Nijar suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa da ayyana dan takarar shugaban kasar na jam’iyya mai mulki a matsayin wanda...
%d bloggers like this: