Yanda tasirin cinikin bayi ke ci gaba da shafar yankin Afrika

Cinikin bayi a Afrika da tasirin da ya haifar.

Yanda ake azabtar da bayi idan an kamo ko ansiyo
Yanda akema bayi bakaken fata daga Afrika.

Yadda tasirin cinikin bayi ke ci gaba da shafar nahiyar Afrika

Cinikin bayi

Yayin cinikayyar bayi zuwa tsallaken tekun Atalantika, miliyoyin ‘yan Afirka ne aka tilasta musu shiga ƙangin bauta.

Akwai labarai da yawa kan muni da ƙazancewar lamarin bautar, har ma da wasu abubuwa na zahiri da suka yi saura game da ita.

A wani kogi da ake kira Donkor Nsou, wato Kogin bauta. a nan ne bayin da suka yi tafiyar sama da mil ɗari uku cikin mari da sarƙa daga arewacin Ghana sukan yi wankan ƙarshe.

Daga nan sai su wuce zuwa gaɓar kogin inda a kan shafa musu mai don jikinsu ya yi kyau.

Kasuwancin bayi: Ana sanya bawa yayi abu dole koda hakan zaiyi sanadin mutuwar sa.

Filin ya kai murabba’in mita 70 faɗinsa, da tsawon mita 80, ana ganin nan ne kasuwar bayi mafi girma a Gold Coast ƙasar Ghana a yanzu.

A wannan waje kuma ana cefanar da mutane kamar wata hajar taba ko goro, wadanda kuma ba a iya sayar da su ba, a kan harbe su ne, saboda sun zama asara.

Bayin da aka saya sai su wuce ta wani gandun daji mai duhuwa zuwa gaɓar tekun Cape da Elmina.

A kan sanya su a ɗakunan ƙarƙashin ƙasa masu matuƙar duhu kafin a zuba su cikin jiragen ruwa zuwa Amurka don aiki a manyan gonaki.

Ana matukar tattalin kogin bauta wanda ke garin Assin Manso na kudancin Ghana, a matsayin wani muhimmin wurin tarihi tun daga 1998.

Divine Azumah Naweh, wani mai yi wa mutane jagora ne ya ce dukkan waɗanda suke ƙasashen ƙetare za su iya samun wata hanya da za ta danganta su da iyaye da kakanninsu.

”Muna da kogin bayi a nan inda za su je su wanke hannuwansu tare da shiga halwa, a lokaci guda suna faɗar abubuwa da dama da suke da burin faɗa wa iyaye da kakannin nasu.

Wasu yankunan duniya

Ita ma Guyana Melissa Noel, ‘yar ƙasar Guyana a nahiyar Amurka ce kuma asali ta fito ne daga Afirka, kuma ta ziyarci wurin a shekarar 2019 a wani ɓangare na shekarar komowa gida Ghana.

”Mun shiga cikin kogin kuma ni da abokai na biyar mun kafa da’ira a cikin kogin. mun yi addu’a, mun yi kuka, na yi kuka sosai, mun godewa magabatanmu, muna alfahari da cewa mun dawo mun yi wanka a cikin kogin inda muka wanke kafafunmu, kakanninmu sun yi wanka na karshe a nan kuma daga nan ba su sa ke dawo ba” in ji ta.

Ta ce wannan wani mahimmin abu ne kuma na ibada wadda ta ke da matukar ratsa zuciya kuma abu ne da bazata taba mantawa da shi ba.

Lokacin cinikin bayi ya shude shekaru da dama amma irin mummunan tabon da ya bari har yanzu ana ganinsa a wannan duniya tamu.

Wuri kamar wannan matashiya ce mai mahimmanci kan irin ukubar da ‘yan Afirkan da aka bautar suka sha.

Yanda ake azabtar da bayi idan an kamo ko ansiyo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here