Yanda Shari’ar Sheikh El’zakzaky ta wakana yau a Kaduna;

Shaida na karshe kuma na goma sha biyar ya shigo kotu. Sunan sa Manjo Janar AK Ibrahim. Ya fara da bayyana cewa a ranar 12/12/2015 yana Kaduna Sai GOC ya kira shi ya shaida masa cewa an tare wa Buratai hanya a Zaria don haka ya umarce shi da tafi Zaria domin yan Shi’a na taruwa. Don haka je ya yi binciken makamai da kuma kamo Shaikh Zakzaky. Ya ce don haka ya tura Laftanar Kanar O. Poul zuwa Husainiya. Ya tura Laftanar Kanar Babayo Darur Rahma. Shi kuma ya nufi Gyallesu. Ya ce sun isa qarfe goma na dare.

Ya ce ya isa Banadeen ya tarar da ‘yan Shi’a da yawa suna cewa Ya Mahdi, Ya Hussain da kuma cewa Allahu Akbar.

Ya ce wasu na dauke da bindigogi qirar gida, wasu da takubba, wasu da gwafa don haka ya fahimci aikin sa zai masa wahala. Ya ce ya yi fatan DA zuwa zai isa gidan Shaikh ya sa shi a mota ya kai shi wurin wadanda suka aiko shi sannan ya yi binciken makamai cikin sauki. Amma da ya kalli yanayin sai ya kira mai gidan sa ya fada masa yadda Gyallesu ta ke.

Don Allah mai gidan sa ya ba shi shawarar ya yi amfani da hanyar da suke bi idan sun je irin wannan aiki.

Don haka ya nemi manyan amsa-kuwwa ya sa aka fara yin shaila cewa kowa ya daga hannunsa sama ya fice daga Unguwar

Ya ce haka suka ci gaba da yi tun ranar asabar har zuwa litinin da safe suka kama Shaikh suka tafi da shi

Ya ci gaba da cewa lokacin da suka fara wannan sanarwar sai wurin ya sake rude wa. Don haka ya ba sojojin sa umarnin su fara motsawa zuwa gidan Shaikh Zakzaky. Tun da suka fara motsawa yan Shi’a suka fara harbin su da duk wani abu da ke hannunsu. Kuma akwai shingaye kamar guda uku kafin a kai gidan Shaikh. An jikkata masa sojoji da dama don haka ya sa aka kwashe su zuwa asibiti daya daga cikin su sunan sa Kofur Yakubu dan Kaduna

In da suka fara kai shi Depot Nigeria Army. Sannan na sanar da GOC game da abin da ya faru da kuma wadanda suka kama. Don haka ya ce to ya jira shi a Zaria gashi nan zuwa. Da ya zo sai ya mika su da makaman da suka kama ga Kanar Ali, wanda shi ne Military Interligent officer shi kuma ya mika su a yan sanda.

Ya ce sun kyale Mata da Yara sun tafi. Amma Shaikh da Matar sa GOC ya tafi da su Kaduna.

Bayan kwanaki uku aka umarce shi DA ya kwashe sojoji ya dawo bariki. Don haka shi abin da ya sani kenan.

Bayero ya tambaye shi ko me ya sa suka yi wannan aikin? Ya ce Saboda tare wa Buratai hanya kuma Gen Usman na wurin ya ce sun yi kokarin ganin Shaikh ya roki yaran sun bude hanya amma Shaikh bai amince ba daga baya kuma ya kashe wayar sa

Marshall ya tambayi Janar ko yana cikin tawagar Buratai? Ya ce yana Kaduna lokacin da abin ya faru.

GOC yana ina lokacin da aka tare wa Buratai hanya? Muna Kaduna tare da shi, Domin a wannan rana Buhari ya zo garin Kaduna. Sai da Buhari ya tafi sannan GOC ya kama hanyar tafiya Zaria kuma yana hanya ne abin ya faru.

Ko ka san Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe Yan Shi’a 347 a bayanan da ta ba da a JCI? Ya ce bai sani ba.

Ko ka ga lokacin da aka harbi Kofur Yakubu dan Kaduna? Ban gani ba

Ya aka yi ka gane wadannan mutanen Shi’a ne? Saboda sun sa bakaken kaya kuma ni babban jami’in Soja ne. Ina da bayanan sirri. Ko kai ma dan Shi’a ne? Domin gashi nan a sa bakaken kaya. Kotu ta rude da dariya domin Janar bakaken kaya ya sa.

Kun tuntubi Yan Sanda kafin ku je Zaria? Yan Sanda sun kasa ne shiyasa muka shigo ciki. Ko kun sami takardar kotu DA ta ba ku umarnin kama Shaikh? Ban samu ba amma rundunarmu ta samu. Ko kai ka kama Shaikh da hannunka? Ba ni bane amma sojojina ne.

Janar kana da masaniyar cewa dukkan mutanen da ka kama a Zaria kotu ta sallamesu? Ban sani ba

Marshall ya kammala tambayoyinsa. Kotu ta tambayi lauyan Malama ko yana da abin cewa? Ya ce ba shi da tambaya

Bayero Dari ya fada wa kotu cewa ya kulle Kes din sa. Abubakar Marshall ya nemi kotu da ta sanya musu rana don yin kariya.

Marshall ya nemi a ba su mako biyu don kawo takardunsu ga kotu. Alkali ya amince da wannan bukata. Don haka nan da kwanaki Sha hudu lauyoyi za su gabatar da takardunsu a rubuce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here