Advert
Home History Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna...

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna (5)

… MABUƊIN ILIMI (5)

MASHI L.G

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna (5)

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Dutsen Bamle Inda ake zuwa Bauta a cikin Kasar Mashi ta jihar Katsina

Bayan munbar Masarautar Zango bamu tsaya ko inaba sai Birnin Dikko, ba don mungama Aikin bincike da ganin Kwaf ba, sai don jiki da jini yana son Hutu, sana kuma dare yayi don wajen karfe takwas da rabi na dare muka shiga cikin Birnin Katsina.

Washegarin Ranar 30 ga watan biyar na miladiyya da misalin karfe takwas na safe, muka kimtsa muka sake komawa gabacin Katsina domin mu ida cimma abinda bamu samu mun cimmasa ba.

Daga Birnin Katsina bamu tsaya ko ina ba sai Gundumar Mashi, a Masarautar Katsina garin Iya Kabir Amin Ibrahim.

Mun isa garin Mashi wajen misalin karfe goma saura mintina goma sha takwas, da isar mu, sai muka yada zango kofar gidan Iyan Katsina Hakimin Mashi, dayake tare da ɗan gari muke (wato ɗaya daga cikin abokan aiki, dan-danan ya shigar da sunan mu ga Hakimi, munyi sa’a Hakimi yana gari, yace “gashi nan fitowa.” Kafin Hakimi ya fito tuni har mun fara aikin mu, da umarnin’yan gida.

Akaimana jagora zuwa cikin gidan Iyan Katsina mukaga abubuwan tarihi mukayi Hotuna, bayan munfito babu jumawa saiga Hakimi yafito, ya tarbemu da farin ciki.

Gaskiya Hakimin kasar Mashi, ya yimana bayani dukda dai ba wani dogon zance yayi ba, amma ya kara karfafamu da shawarwari akan aikin da muke; sannan ya kara hannunta mu ga Abokin aikin namu yace “Shi dan gida ne, zai mana jagora duk inda muke buƙatar zuwa a ƙasar Mashi.

Mukayi godiya muka fito. Fitowar mu keda wuya Abokin aikin namu yace “Bamle Zamu nufa” Wani kauye me nisan kimanin Mil ashirin zuwa ashirin da biyar, kauyen yayi iyaka da ƙasar Kaita ta wajen Dankama, Sannan yayi iyaka da ƙasar Nijar, Munga Dutsen Bamle, Munga Dutsen Fata, Duwatsu masu dauke da Abin mamaki, Lallai ance Tsafi gaskiyar maishi, Zamu baku labarin abinda muka gani a tattare da Dutsen, dama abinda maguzawa sukayi, kuma sukeyi a wajen Duwatsun, a

www.katsinacitynews.com

Muna da Bidiyo da muka Dauko da tarihin Dutsen a tashar mu ta Youtube Channel a KATSINA CITY NEWS TV

Ko kuma ku sauke Manhajar mu a wayoyin hannun ku ta Play Store

Katsina City News

Daga Dutsen Bamle Sai ina kuma?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: