Advert
Home Sashen Hausa Yanda Muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna....

Yanda Muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna. (3)

… MABUƊIN ILIMI (3)

Yanda Muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanan Tarihi da Hotuna. (3)

BABBAN MUTUM 

Zaharaddeen Mziag @ Katsina City News

Bayan Mun kwashi Tarihi da Hotuna a Masarautar Ɓaure; sai muka ƙara Nutsawa ƙarshen Najeriya ta Gabas, wato Wani Gari da yayi iyaka da Jamhuriyar Nijar daga ɓangaren Arewaci a ɓangaren, yayi iyaka da Jihar Jigawa daga Ɓangaren kudanci.

Garin Babban Mutum shima yana cikin Masarautar Daura ta jihar Katsina kuma tanada Hakimi.

Dama a ƙa’idar aikin namu dole ne mu zamo masu haƙuri da ɗaukar ko wane irin hali da muka tsinci kammu a ciki, kuma Bahaushe yace Asiya a faɗi gaba akayi.

Isar mu garin Babban Mutum Munshiga cikin sa’a Amma ba ta abinda mukaje nema ba, bayan mun tambayi gidan Hakimi an nuna mana, mun iske wani Dattijo a kofar Fada zaune yana shan Iska, muka gaisa gami da gabatar da kanmu dakuma abinda ke tafe damu. Yaji daɗi sosai kuma yayi mana Sannu da zuwa, Yace “Hakimi ba nan yake zaune ba, Amma bari ya kira mana wakili” muk jira bayan wasu ‘yan mintina sai gashi ya dawo yace mana gashi nan zuwa.

Ba’a kasa Mintina goma ba sai ga wani Dattijo wanda har muka baro garin bansan sunansa ba, bayan ya iso cikin girmama muka gaisheshi kuma muka gabatar masa da takarda game da buƙatar mu.

Dattijon ya amsa ya fara karantawa sana yayi shiru na tsawon lokaci, har takaiga saida mukace “ko baku da kayan tarihi a nan garin Babban Mutum?” Dattijo yace “a’a ace babu bari dai inzo”! Yatashi ya nufi Yamma kusa da inda muka aje Motar mu, dayake akwai wasu Samari a cikin wata Rumfar Haki a wajen, da wani ɗan gini me kamada akurkin kaji, naga an rubuta (Out Post Babban Mutum) hakan yasa nayi tunanin “Police station ce”, ammafa wajen a rufe yake.

Muna nan zaune shima andaɗe sai gashi ya dawo yacemana “Ba ni yakamata ku gani ba wanda yakama kugani yaje Ɗaurin Aure, ku ɗan jira yanzu zai dawo. Mukace to muna neman Izinin wucewa zuwa gaba wani lokaci zamu dawo, saboda busa hanya muke, “yace ai bai kamata mutafi ba bayan munsha doguwar tafiya, mudai jira yazo don yafishi sanin duk inda yakamata aje.” Mukayi biyayya muka jira, shidai be cemana uffan ba muma haka, saboda a fahimta ta ba mutum bane me son surutu.

Can bayan wani lokaci kaɗan sai mukaji kiran Sallar Azuhur, mukace bara muyi Sallah “Dattijo yace haka yakamata bari a samo Ruwa” muka ɗan jira shiru Dattijo be kawo mana ruwa ba kuma be aiko ba, dama da Ruwan mu muke tafe a cikin mota, muka fiddo mukayi Al’wala, kafin mushiga Masallaci sai na hangi wannan Dattijo yayi Al’wala ya shige Masallaci abinsa (nayi tunanin ya hangi mun samu ruwa munyi Al’wala ne shiyasa bai kawo mana ruwan ba) muma muka shiga Masallacin mukayi Sallar Ƙasaru dayake na riga abokan tafiyar nawa fitowa daga Masallacin ina tsaye a kusa da wani Iccen Bedi sai ga wannan Dattijo yafito dama hikimar kenan inmasa magana ni kadai, don inji idan abinnan mai yiyuwa ne. Kafin ma inyi masa magana sai naga ya tunkaro ni shi da wani, wanda a yanayin shekaru shi Dattijon ya girmi wancen, muka ƙara gaisawa dasu su duka, sai Dattijon yace wannan shine wanda muke jira shine wanda zai nuna maku wuraren da kuke nema a madadin Hakimi, nayimasa sannu da zuwa, yace “Daga Ɗaurin Aure ya dawo, bari yaje ya kimtsa yayi Sallah sai ya fito” nace afito lafiya Ranka ya daɗe! Nidai tun daga wannan lokacin ban kuma ganin ko walkiyar Rigarsu ba, abokan tafiya suka fito muka sake wani sabon jiran, har muka sayi fura aka dama mana muka sha, babu su babu dalilin su, daya daga cikin abokin aiki ya samu lambar hakimi ya kirashi, ya fara gabatar da kai, amma saboda ƙarancin Network ba aji sosai, a haka muka kwashe ya namu-ya namu muka bar garin Babban Mutum, ba tare da munsan tarihin koda kazar garin ba, balle Wani Babban Mutum ko wasu muhimman wurare idan akwai, don haka a kundin mu na taskace Tarihi ta’iya yiyuwa Babu Babban Mutum koda yake bayan tafiya tayi nisa Hakimi ya kira wayar abokin Aiki yana bada haƙuri, bansani ba ko zamu koma.

Wannan shine Abinda ya faru damu a Babban Mutum, dama dai ma’abota Hausa a Dunƙule sunce ba Kullum ake kwana a Gado

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANZU-YANZU: Darakta-Janar na Inuwar Gwamnonin APC ya ajiye muƙamin sa

Darakta-Janar na Inuwar Gwamnonin APC, Salihu Lukman ya ajiye muƙamin sa. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ajiye muƙamin na sa na da nasaba da rikicin...

THE M.K.O. ABIOLA NATIONAL STADIUM IN ABUJA HAS BEEN SUCCESSFULLY REHABILITATED!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/257296063153585/

RASHIN TSARO: Attajiri Aminu Dantata ya fashe da kuka…

Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya Ta Yi Silar Zubar Da Hawayen Aminu Dantata Yayin Gudanar Da Taro Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata...

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...