Advert
Home History Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren...

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren Tarihi da Hotuna.

… MABUƊIN ILIMI (1)

SANDAMU L.G

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren Tarihi da Hotuna.

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Tun daga Dankama har Damari babu inda bamu taka ba muka ganewa idanuwan mu wasu muhimman wuraren tarihi da bayanan su.

Ga ɗan Asalin jihar Katsina Idan nace tun daga Dankama har Damari yasan me nake nufi, ga baƙo kuwa Ina nufin daga farkon Jihar Katsina zuwa karshen ta, acikin rubutun mu da zamuyi game da Muhimman wuraren tarihi a ƙasar Katsina zakuji Ina ne Dankama Inane Damari.

A ranar Asabar ta 29 ga watan Mayu na Shekarar dubu biyu da ashirin da daya 2021 ranace da ba zan taba mantawa ba, saboda rana ce da muka sanya ɗan, ba” na zagaye ƙasar Katsina me Jimlar kilomita Dubu Ashirin da huɗu da ɗari ɗaya da casa’in da biyu (24192km) cikin kwanaki goma sha biyu.

Tabbas Tafiya Mabuɗin Ilimi ce, ballantana Irin tafiyar mu ta bin diddiƙi ganin kwaf, da kwalailaita.

Misalin karfe takwas na safe muka bar Katsina dani da Abokan aiki, muka nufi Gabacin Jihar Katsina, Muka shiga ƙasar Mashi, muka fita Daura, bamu tsaya ko ina ba sai a karamar hukumar Sandamu, a gidan Hakimin Sandamu wato Ɓunturawan Daura Alhaji Ya’u Sani Zakari. Mutumin Kirki me son jama’a (Me hannun kyauta) Kamar yanda naji daga cikin Talakawan sa na kiran sa. Alokacin da muka sauka a Fadar sa, baya nan yaje gona, sai muka sanar da waɗanda muka gani a kofar gidansa daga Inda muke, nan take wani Matashi da ban tambayi sunan sa ba, yace mubari a kira mana shi da waya, mukace ya bari zamu jirashi, wani Dattijo dake gefe zaune yace ai yanzu kun ganshi, Shi kuma wannan matashi ashe harma ya kira wayar maigirma Ɓunturawa, bayan sun gama waya matashin nan yace mana “Ai gashi nan busa hanya” ba’ayi cikakken mintuna uku ba sai ga Motar Pijo 406 ta tsaya, Hakimi ne dashi da Ɗan’rakiyarsa.

Cikin fara’a da murna muka gabatar da kammu da takardar da mukazo da ita zuwa gareshi, ya amsa Hannu biyu ya jamu a fadarsa muka kwashi tarihin Garin Sandamu daga bakin mai girma Ɓunturawan Daura, da kansa da kafarsa ya taka zuwa wasu muhimman wurare na Tarihi hadda tsohon gidan Sarautar Sandamu da ya kwashe ɗaruruwan Shekaru. Munyi cikakken bayanin abinda muka gani Asalin su tarihin su da Hotuna da Bidiyo, a shafin mu na KATSINA CITY NEWS wato www.katsinacitynews.com

Domin ganin Bidiyo sai ku ziyarci tashar mu ta Youtube Channel KATSINA CITY NEWS TV

Munada Manhaja ta Application da zaku iya saukewa a wayoyin hannun ku daga Play Store domin ganin aikace aikacen Katsina City News da Sauran Abubuwa. Bayan Hakimi ya gwargwada mana abubuwan Tarihi, da taimakon wasu dattawa kuma ya Dauko Alheri yayi mana ya rakamu har wajen mota cikin farin ciki mukayi bankwana. Lallai Ɓunturawan Daura Hakimin Sandamu bashi da girman kai irin na sauran sarakuna.

Daga nan sai ina? Tawagar binciken Kwakwaf na kayan tarihin ƙasar katsina bata zame ko ina ba sai Karamar Hukumar Baure, Gazawa Namijin Gari ta Abdu kowa Maina.!!!

Mi ya faru damu a Garin Ɓaure? Ina muka leƙa mi muka gani, sai ku biyomu a rubutu na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: