Advert
Home Sashen Hausa Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren...

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren Tarihi da Hotuna (6)

… MABUƊIN ILIMI (6)

MAI ADUA L.G

Yanda muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren Tarihi da Hotuna (6)

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Daga Dutsen Bamle sai ina kuma?

Bayan munyi abinda mukayi, munga abinda muka gani a Dutsen Bamle, sai muka baro garin Bamle, muka hau hanya ɗoɗar, duk da dai hanyar ta matuƙar lalacewa (don bazakayi tafiyar sakan talatin ba ba tare da ka faɗa rami ba) amma hakan bai hanamu bin hanyar ba, saboda ita kaɗaice zata sadamu da inda zamu nufa.

Ta Kauyen Baranzama muka bi, muka fada Shekiyal, muka ɓulla Bum-Bum, mukabi ta Galadimawa sai gamu cikin Ƙasar Mai Adua’a Masarautar Daura, duk da Mun leƙa Safke wani kauye ne dake da Dam ɗin Noman rani me ban sha’awa da Dausayin Noma, tabbas a Safke Dam munga abin shawa, munga tashar Ruwa yanda ruwa ke shiga lungu da sako na gonaki domin su inganta Nomansu, Mun isa wajen alokacin da ake tsumayin Ruwan Damuna, wataƙil shiyasa bamuga kayan lambu ba, amma idan ba don wannan hasashen ba da sai ince “waje ne ga Ruwa ba noma” shima mun dauki Hotuna da Bidiyo zamu kawo maku su a www.katsinacitynews.com dakuma tashar mu ta Youtube Channel KATSINA CITY NEWS TV. Mun isa Mai Adua a ranar ta Lahadi ranar da kasuwar garin ke ci, bamu zame ko inaba sai ƙofar gidan Galadiman Daura Hakimin Mai adua Alh. Amadu Diddiri Amadu.

Bayan mun isa muka sauka a fadar Galadima aka isar masa da sakon mu, bayan wani ɗan lokaci sai Galadima ya Aiko aka shigar damu cikin gida don Karramawa, muka iske shi, zaune a Falon sa mukayi gaisuwa, muka ƙara gabatar da kanmu dakuma abinda ke tafe damu. Me girma Hakimi yayi farinciki da zuwan mu, kuma yabamu tarihin Masarautarsa ta Mai adua, asalin kafuwarta dakuma al’adun mutanen mai Adua, harda wata tsohuwar rijiya da take da ɗinbin Tarihi. Me girma hakimin mai Adua mutumin kirki ne me son jama’a kuma bashi da girman kai, don kuwa bayan mun gama tattauna abinda ya kawo mu, sai muka kashe na’urar naɗar magana, mukaci gaba da Taɗin Duniya, Alh. Amadu Diddiri yasan (Source of Revenue) yanda yakamata don mun tattauna dashi akan wannan (amma a bayan Fage ba acikin aikin mu ba) daga nan mukayi bankwana yayo mana rakiya har bakin kofa, yakuma haɗamu da wanda zai gwadamana Rijiyar Dandali me tarihi, mukaje mukayi Hotuna, sana muka shiga kasuwa nan ma mukayi hotuna, muka sha Fura mukaci Nama, muka nemi hanyar gaba. Zamu kawo maku Tarihin Mai Adua da Rijiyar mai adua dama bidiyo akan ziyarar a www.katsinacitynews.com

Da Youtube Channel KATSINA CITY NEWS TV. Daga Mai Adua sai ina?

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Likitocin ƙwaƙwalwa da dama na barin Nijeriya, Malamin jami’a ya yi gargaɗi

Farfesa ilimin ƙwaƙwalwa, Farfesa Taiwo Sheikh ya ce ɓangaren likitocin ƙwaƙwalwa shi ne ya fi samun naƙasu a ɓangaren ƙarancin likitoci da ke faruwa...

Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da a ka binne Hanifah

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da a ka binne Hanifah Gwamnatin Nijar Kano ta bada umarnin rufe Noble Kids Academy, makarantar kuɗi da ke...

Kwazo Tunani da Hangen nesa yasa mukaga dacewar ya zama Gwamnan jihar Katsina.  -Alliance for Democracy and Purposeful Leadership- ga Sanata Sadiq Yar’Adua

Kwazo Tunani da Hangen nesa yasa mukaga dacewar ya zama Gwamnan jihar Katsina.  -Alliance for Democracy and Purposeful Leadership- ga Sanata Sadiq Yar'Adua A ranar...

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a wani Sansanin Soji dake Shimfiɗa, ƙaramar Hukumar Jibiya ta jihar Katsina

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Sansanin Soji A Katsina ’Yan bindiga sun kashe wani soja da wani jami’in Rundunar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC)...

PHOTO NEWS: President Muhammadu Buhari(GCFR ),has commissioned the newly remodelled Murtala Muhammad Square

President Muhammadu Buhari(GCFR ),has commissioned the newly remodelled Murtala Muhammad Square. #PMBinKaduna #KadunaUrbanRenewal