Yanda Muka zagaye Jihar Katsina domin tattara Muhimman bayanai game da wuraren Tarihi da Hotuna (2)

…MABUƊIN ILIMI (2)

BAURE L.G

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News.

A ci gaba da zagaya ƙasar Hausa wato ƙasar Katsina a ranar Asabar 29 ga watan Mayu, bayan munbar ƙasar Sandamu a Masarautar Daura bamu tsaya ko inaba sai Garin Ɓaure, duk a cikin Masarautar Daura ta jihar Katsina

*Ɓaure Gazawa namijin gari ta Abdu Kowa Maina*

Bayan isar mu kofar Fada bamu iske kowa ba, sai muka yi kokarin yin Sallama, saboda motsin mutane da mukaji daga cikin fadar, akayi sa’a wani magidanci ya fito hannunsa da alamun ruwa; yana wanki ne, ko ban Ruwa.

Bayan ya fito muka gaisa, sannan muka gabatar da kammu da kuma inda muka fito, sai ya faɗimana cewa “Ai hakimin Ɓaure ba a Ɓaure yake zaune ba yana Daura, sai dai wakilin Hakimi.”

Mukace anyi dai-dai kenan, munaso a sada mu da shi, ya yarfe hannunsa ya goge a riga, sana ya ida fitowa daga ciki; dama yana daga cikin Zauren Masarautar mu kuma muna daga waje.

Yayi gaba muka bishi a baya, tafiyar bata gaza tsawon mita goma sha biyar ba kusa da gindin Iccen Bedi da wata rumfar haki, wani Dattijo me ɗan kaurin jiki zaune busa tabarma da baƙin gilashi (tubarau) a fuskarsa, bayan mun isa muka gaishe shi, sana muka gabatar da kammu dakuma daga inda muka fito.

Dattijon me suna Alh. Ali Adamu Sarkin Fulanin Ɓaure (Wakilin Hakimin Ɓaure) ya karɓemu hannu bibbiyu, kuma munsha tarihi, ankuma Gwadamana wajajen tarihi na Ƙasar Ɓaure, inda magatakarda ya jagorance mu zuwa ko’ina lungu da sako, na ƙasar baure munga daɗaɗɗin kayan tarihi, a Masarautar Ɗan Buram Daura Hakimin Ɓaure Alhaji Ɗaha Umar Farooq Umar. Munyi Hotuna da Bidiyo.

Zamu kawo maku dukkanin bayanin Asalin ƙasar Baure tarihin ta da masarautar gami da wasu muhimman wurare a ƙasar, ku biyomu a www.katsinacitynews.com

Da Youtube Channel din mu na KATSINA CITY NEWS TV

Ko ku sauke Manhajar mu ta Application a Play Store a wayoyin ku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here