YADDA APC KE YAKAR KANTA DA KANTA

…Misali daga Karamar Hukumar Rimi

@ Katsina City News

Karamar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina na daga Kananan Hukumomin da suke ga baki ga hanci da babban birnin Jihar Katsina. Don haka wayewarsu a ilmance da siyasance tana da fadi da karfin gaske.

Suna da fadin kasa da yawan jama’a da fitattun ‘yan kasuwa, ‘yan boko da gogaggun ‘yan siyasa, kusancinsu da birnin Katsina ya kara buda masu idanu.

Yadda APC ke tafiyar da ba da mukaman alfarma da na siyasa a Karamar Hukumar, kamar tana yakar kanta da kanta ne. Abun ba lissafi ba hangen nesa.

Rimi tana da rumfar zabe guda 134, amma duk an tattara mafi yawan mukaman an kai yankin da ke da rumfuna 14, shi ne garin Abukur.

Cikin mukami tara da Karamar Hukumar ke da su, shida duk suna a Abukur.

Dan Majalisar Jiha daga Abukur, Shugaban Hukumar KASROMA daga Abukur, Kwamishinan dindindi daga Abukur, Shugaban ma’aikata na Karamar Hukuma daga Abukur, Shugaban kudi da gudanarwa na Karamar Hukuma daga Abukur da Unit Head Abukur.

Wasu manyan ayyuka da yanzu ake yi a garin yana rura wutar gabar siyasa a Karamar Hukumar.

Ayyukan sune aikin hanyoyi da Hukumar KASROMA ke yi a garin na Abukur, mutanen Rimi cewa suke su ya kamata a yi masu, domin duk inda ake wannan aikin ana yi ne a babbar hedikwatar Karamar Hukuma, a Rimi ne kawai aka karkatar zuwa Abukur. Dan Majalisar Jiha ya kai wani aikin na hanya da shataletale a Abukur. An tattara manyan ayyuka biyu duk an yi su a Abukur.

Babban abin da ya kara fusata mutanen sauran bangaren a siyasance shi ne, ba da mukamin DAF ga wani dan Abukur, wanda ya cancanta a ba shi ne; Alhaji Isiyaku Karare tsohon ma’aikacin Karamar Hukuma ne wanda yanzu yake matsayin Darakta.

A baya Isiyaku Karare ya taba rike shugabancin Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina, wanda ya yi aikin da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, shi ne Maigarin Karare a Karamar Hukumar Rimi, kuma an shaide shi a iya tafiyar da mulkin garinsa bisa adalci.

Karare yana da mutunci a Ma’aikatae Kananan Hukumomin Jihar nan sosai, yana da kima a Katsina, adalcinsa ya sa mutanensa na son shi, don haka a Rimi ake alfahari da shi.

A farko an tabbatar za a ba shi, amma cikin shige da fici na rashin lissafin siyasa mai kyau aka canza sunansa da wani daga Abukur da bai kai shi ba.

Idan shugabannin jam’iyya, musamman daga Jiha kansu kawai suka sani da abin da zai zo masu, sukan zama ba ruwansu da lissafin raba mukamai yadda zai je ga kowane bangare, har a yi adalci, kuma a samu daidaita suka canza maganar.

Jam’iyya ta samu shugabanni marasa hangen nesa da son rai na da daga cutar kansa a gare ta, in ji wasu da muka zanta da su a garin.
_______________________________________________
Jaridar Katsina City News na bisa yanar gizo www.katsinacitynews.com da Twitter. You tube da kuma sauran shafukan yanar gizo. Duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here