Yanda aka kama Abdulrashid Maina a Jamhuriyar Niger

Abdulrashid maina yashiga komar jami'an tsaro

An kama Abdulrasheed Maina a Nijar

.

Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa wani babban jami’in tattara bayanan sirri ya shaida mata cewa an samu nasarar kama Maina ne sakamakon irin danƙon zumuncin da kuma yarjejeniya ta tsaro da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Abdulrasheed Maina, wanda tsohon shugaba ne a kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, na fuskantar tuhume-tuhume har guda 12 tare da wani kamfani, inda hukumar EFCC ce ta gabatar da tuhume-tuhumen a kansu.

EFCC na zargin Maina da amfani da asusun wani kamfani wajen halatta kuɗin haram har kusan naira biliyan biyu, wanda cikin kuɗin ne ake zargin ya sayi wasu kadarori a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here