A ci gaba da aikin gyaran ruwan cikin birnin Katsina da kewaye, a yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya zagaya wuraren da muhimman ayyukan suke gudana tare da manema labarai domin gane ma idanuwan su yadda aikin yake samun ci gaba. Haka kuma Gwamnan ya duba wasu ayyukan hanyoyi a nan cikin gari da kuma Kaita.

A babbar tashar halba ruwa dake Kofar Kaura, Gwamnan ya duba injin samar da wutar lantarki mai karfin KVA 800 wanda zai rika ba tashar isassar wutar da za ta ishi manyan famfuna masu halba ruwa zuwa cikin gari, musamman manyan tankunan Rafindadi, rawun na steel rolling da kuma na kankare dake hanyar Dutsinma.

Wannan tasha za ta rika halba ruwan da zai taho daga Ajiwa da kuma Zobe.

Haka kuma, an kawo sabbin famfuna guda shidda da za su maye gurbin wadanda suke wurin a halin yanzu. Wadannan famfuna da aka kafa tun cikin shekarar 1974, an gama cinye moriyar su har ta kai wasun su sun tsaya, masu motsin kuma bai biyan bukata.

A babbar tashar samar da ruwan kuwa dake Ajiwa, Gwamna Aminu Masari ya duba manyan Injunan samar da wutar lantarki masu karfin KVA 2000 ko wannen su, wanda su ne za su rika samar da wutar da za a rika aikin tacewa da kuma halbo ruwan zuwa tashar dake Kofar Kaura. Wanda kuma tuni aka kammala aikin kafa sabbin famfunan da za suyi wannan aiki.

Wadannan injuna tuni an gwada su kuma suna aiki yadda ya kamata, kuma idan Allah Ya kai mu Laraba wakilan kamfanin da suka kera Injunan za suzo daga kasar Jamus domin mika aikin ga hukumar ruwa ta jiha.

Gwamna Aminu Bello Masari ya nuna gamsuwa da ingancin ayyukan da ake yi tare da cewa da yardar Allah zuwa karshen wannan shekara ayyukan za su kammala. Haka kuma, Gwamnatin Jiha tana kan shirye shiryen bada kwangilar fadada madatsar ruwa (Dam) ta Ajiwan domin kara yawan da take samarwa.

Shugaban kamfanin Continental dake aikin kwangilar Alhaji Salisu Mamman shi ya zagaya da Gwamnan wajen duba wadannan ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here