YANDA ƳANSANDA KE GARKUWA DA MUTANE DON NEMAN KUƊIN FANSA.

Saida suka amshi Naira miliyan ɗaya da dubu hamsin kana suka sakeni, inji Abubakar ɗan Haɗeja

YANDA ƳANSANDA KE GARKUWA DA MUTANE DON NEMAN KUƊIN FANSA.

Zaharaddeen mziag @katsina city news

Babban Abin damuwa ga Mutanen Arewacin Nigeriya a yanzu shine yanda ake sace su domin neman kuɗin fansa, wato (Kidnapping) wan’nan mummunan aiki ba ga ɓarayin daji masu garkuwa da mutane kawai ya tsaya ba, hatta acikin jami’an tsaron ƴan sanda abin ya shiga. Domin kuwa ansamu wasu ƴan sanda masu tasowa daga Abuja su shigo Kano, da nufin gudanar da aiki, sai su haɗa kai da wasu jami’an (abokan aikin su) dake kano suna garkuwa da mutane mai lasisi.

Ƴan sandan sun haɗa wani gungu da yake aiki irin na masu garkuwa da mutane, yanda suke wan’nan mumunan aikin kuwa shine; suna shiga ƙauyuka da kasuwannin fulani suna zaɓar wanda tsautsayi ya faɗawa, su cafke su sukawo su kano su killace su a Ofishin ƴan sanda na kwakwaci, sannan sunemi akawo maƙudan kuɗaɗe kafin su sake su.

Wan’nan muguwar ɗabi’ar ta yin garkuwa da mutane mai lasisi ta daɗe ana yinta, inda wasu ƴan sanda ke amfani da Offishin ƴan sanda na Dala ko na Sharaɗa domin gudanar da wan’nan aiki nasu.

Kamar yanda shirin Inda ranka na gidan Radio freedom ya gano Ofishin ƴan sanda na kwakwaci shine babbar makillata, wanda bin diddiƙin wakilin gidan Rediyon  ya yi shigar ɓadda sau domin ya ganewa idon sa, inda yagano yanda ake tsantsar kasuwanci kuma a tsanake, idan kaje duba ɗan’uwanka za’aimaka kuɗi kabiya sana katafi dashi.

Kamar yanda wakilin Rediyo freedom yace wan’nan fa babbar magana ce mai tsaurin faɗi wanda idan akaci gaba da yimata riƙon sakainar kashi zata iya jawoma jihar matsala dama ƙasar baki ɗaya.

Wani bafulatani Abubakar garba da Freedom suka tattauna dashi yace, Ammasa haihuwa don haka yakama maraƙi yaje kasuwar kwanar ɗan gora domin ya siyar, kan hanyarsa ta dawowa bayan ya karɓo kudin sa sai kawai yaji an cakume shi daga baya, koda ya waiga sai yaga wani ɗan sanda mai suna Abdullahi Barumi, a ƙarshe Barumi yasanya masa Ankwa yakaishi Offishin na kwakwaci ya killace shi.

Bafulatani Abubakar Garba yace saida ya shafe kwanaki Ashirin da ɗaya a kwakwaci kafin daga bisani aka haɗa sama da naira dubu ɗari hudu aka fanshe shi.

Wani abu dake tayar da hankali shine akwai wasu mutane biyu da ake zargi sune sukeyin cune idan sunga fulani sun samu kuɗi, kuma idan aka kama mutum sune masu zuwa wajen dangin suce a haɗa kuɗi abasu suje su fanso su daga wajen ƴan sanda a kwakwaci, kamar yanda suka karɓo Abubakar, haka ma dai sune suka karɓo wani Abubakar ɗan Haɗeja, wanda ƴan sandan suka kama sai da ya biya kuɗin fansa naira miliyan ɗaya da dubu hamsin. Kamar yanda ya bayyanawa Freedom rediyo. “Ina gida da safe sai wani ya kirani ta waya yace inzo bakin hanya yanason ganina danazo sai naga ƴan sanda a take suka kamani suka ce Abuja zasu wuce dani, kuma daga baya sai suka dawo dani suka zo nan kwakwaci suka ajeni saida nayi kwana ashirin da biyu a hannun su, wai ana neman Nagge Sittin hannu na da bindiga, sannan sukace idan munkoma gida inbasu haɗin kai duk wani wanda nasan yanada wani abu zasu sa akama shi kuɗin da suka ɗoramin sai naci riba, nafarko sun karɓi naira dubu ɗari shida da ashirin bayan sunfidda ni natafi gida washe gari sukazo suka amshi naira dubu ɗari huɗu, kuma alokacin da suka kamani a kwai naira dubu talatin da shida a hannuna” Inji ɗan Haɗeja.

A bayyane yake cewa su kansu masu garkuwa da mutane na cikin daji sukan karɓi miliyan ɗaya koma ƙasa ga haka, amma gashi nacikin birni suma farashin su yakai naira miliyan guda harda naira dubu hamsin kamar yanda ɗan Haɗeja yace haka aka karɓa a wajen sa.

Akwai wani ɗan sanda mai suna sufeto Sada, wanda shine jagoran waɗannan ƴan sanda na Abuja dake zuwa su yada zango a kwakwaci, Rediyo freedom ya tuntuɓeshi inda ya musanta zargin, amma yace yasan anzargi yaron sa Audu Barumi da karɓar waɗan’nan kuɗaɗen, kuma yace ai anje gaba, har anɗauki mataki harma am mayar wa da fulanin kuɗaɗen su, yanzu haka maganar dawoma waɗan nan fulani kuɗaɗen su tana cen a sashen ISB na rundunar ƴansandan jihar kano.

Aɓangaren hukumar ƴansandan na kano tace tananan ta faɗaɗa bincike kuma zata sanya ƙafar wando ɗaya da duk wanda aka samu da hannu cikin wan’nan muguwar ɗabi’ar.

A inda al’uma suke ganin lallai akwai babban haɗari ace ƴan sanda kawai su shigo daga Abuja su sauka a Kano suna damƙar mutane suna barazanar kaisu Abuja, amma dazarar kabiya kuɗi shikenan ka fanshi kanka baza a sake cewa kayi laifi ba, dafatan mahukunta zasu duba kuma su ɗauki kwakwaran mataki, suma masu motoci sunce ana yawan kamasu ace za akaisu Abuja sai kawai a wuce dasu Dala a tsagaga masu kuɗi don su fanshi kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here