GGSS Jangebe: Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 a jihar Zamfara

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan ‘yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

Kabiru sani, mataimakin shugaban Muryar Talaka ta jihar Zamfara, wanda aka sace ‘ya’yan dan uwansa uku, ya shaida wa BBC Hausa cewa yanzu haka sun shiga daji domin bin sahun ‘yan bindigar.

Haka kuma wani mutum da aka sace ‘yarsa daya mai suna Bilkisu da ‘ya’yan ‘yan uwansa biyu, ya ce daruruwan ‘yan bindiga ne suka isa makarantar inda suka soma da kai hari kan masu gadi kafin su yi awon gaba da daliban.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Sace-sacen ɗalibai a makarantu huɗu da suka girgiza Najeriya
Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ‘yan fashin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

BBC na ci gaba da samun ƙarin bayani a kan wannan labari na Zamfara, za mu sanar da ku ci gaban da aka samu…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here