Jigawa: ‘Yan bindiga sun kashe manyan jami’an ‘yan sanda biyu a Jihar

ASALIN HOTON,GETTY IMAGE
Wasu miyagu sun kashe manyan jami’an ‘yan sanda biyu a Ƙaramar Hukumar Garki da ke Jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdu Jinjiri, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a yayin da miyagun suka yi wa jami’ansu kwanton ɓauna a wata rugar Fulani da ke yankin.
DSP Jinjiri ya ce sun yi nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan a musayar wutar da ta biyo bayan harin.
‘Yan sandan da aka kashe sun haɗa da mai muƙamin DSP da kuma SP tare da jikkata wani mai muƙamin kurtu, a cewarsa.
Kazalika ya tabbatar cewa sun ƙaddamar da harin ne kan ‘yan bindigar sakamakon sace wata ɗalibar Jami’ar Sule Lamido da ke jihar, wadda ya ce maharan ne suka sace ta.
Ƙasa da mako ɗaya kenan maharan suka kashe ɗan sanda ɗaya yayin da suka sace ɗlibar wadda aka bayyana da suna Zainab Isa Zakari a Ƙaramar Hukumar Maigatari ranar Litinin.
“Bayan wasu bayanan sirri da muka samu, mun gano cewa akwai maɓoyar masu garkuwa da mutane a garin Kargo a Ƙaramar Hukumar Garki, waɗanda suka uzura wa Masarautar Gumel,” in ji DSP Jinjiri.
“Wannan dalilin ne ya sa ofishin ‘yan sanda na Gumel ya shirya wani samame ranar 25 ga Disamba da tsakar dare kuma suka dirar wa wurin.
“Abin baƙin ciki sai miyagun suka buɗe wa ‘yan sanda wuta daga wurin da suke ɓoye, abin da ya jawo harbe-harbe. Miyagun sun kashe mana manyan ‘yan sanda biyu da kuma raunata wani ƙarami. ‘Yan sanda ma sun kashe ɗaya daga cikin miyagun.”
A ‘yan kwanakin nan masu garkuwa da mutane na ƙara karaɗe jihohin arewa maso yamma, inda ranar Talata wasu ɗauke da makamai suka sace wani attajiri a garin Minjibir na Jihar Kano bayan sun ƙone motar ‘yan sanda.