‘Yan wasan Wikki Tourists ta Bauchi sun yi hatsari

Motar ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourists ta garin Bauchi ta kama da wuta a yau Alhamis yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Akwa Ibom.

Ƙungiyar mai buga Firimiyar Najeriya na kan zuwa filin wasa na Godswill Akpabio International da ke garin Uyo domin karawa da ƙungiyar Dakkada a wasan mako na 11 ranar Lahadi.

Wani bidiyo da ɗan wasan Wikki, Damala Ezekeil, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna yadda motar ke ci da wuta a gefen titi.

“Lamarin ya faru ne a safiyar nan a garin Hawan Kibo a kan hanyarmu ta zuwa Akwa Ibom…tayarmu biyu ta fashe kafin motar ta kama da wuta,” a cewarsa.

Sai dai sun auna arziki domin kuwa babu wanda jikkata balle rasa rai.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here