Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mata sama da 30 sakamakon hare-haren da suka kai kauyuka 15 a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

A cewar wani rahoton sashen Hausa na BBC, wasu mazauna kauyukan Geba da Gidan Kaura, da kuma wasu yankunan Gusau, sun ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummarsu, sun kashe mazaje tare da lalata dukiyoyi.

“‘Yan bindigar sun sace mata da ‘yan mata, sun tafi da su,” in ji su.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mata 10 a Kura da tara a Bayauri. “Sun kuma shiga wani kauye mai suna Gana suka yi garkuwa da bakwai kafin su wuce Duma suka yi garkuwa da wasu bakwai. Wadannan sun faru ne kafin safiyar Lahadi.”

Rahoton ya kara da cewa kauyuka da dama sun zama ba kowa, yayin da mazauna kauyukan ke tashi da gudu zuwa Gusau babban birnin jihar.

Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da cewa an kai harin ne a Geba, inda ya kara da cewa jim kadan bayan harin jami’an tsaro sun je kwantar da hankula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here