‘Yan Shi’a Mabiya Alzakzaky Sun Sake Jaddada Kiran A Saki Malaminsu A Katsina.

Daga Wakilin mu

Da safiyar yau Asabar 2 ga Janairu 2021, ‘yan shi’a mabiya Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky suka sake yin gagarumin jerin gwano a jihar Katsina, inda suka jaddada kiranye ga gwamnatin Najeriya na cewa lallai ta sakar masu Malami haka nan.

Jerin gwanon wanda ya fara daga Unguwar Filin Polo ya biyo ta kofar ‘yandaka sannan ya tuke a Unguwar Madawaki.

Ana dai ci gaba da tsare Malam Ibraheem Alzakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatu tun watan Disambar 2015, duk da umurnin da babbar Kotun tarayya ta yi na cewa a sake shi sannan a biya shi diyyar tsarewar da aka yi masa, amma dai gwamnati ta yi kunnen uwwar shegu da umurnin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here