Advert
Home Sashen Hausa Yan Shi'a: Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ke dakile 'yancin...

Yan Shi’a: Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ke dakile ‘yancin yin addini

Yan Shi’a: Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ke dakile ‘yancin yin addini

A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta kama shugaban mazahabar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky
Bayanan hoto,Amurka ta ce gwamnatin Najeriya ba ta bari a gudanar da addini yadda ya kamata

Gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke dakile ‘yancin gudanar addini.

Kasar ta ce Najeriya tana barazana ga masu son yin addinansu kamar yadda ya kamata.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, bai bayar da dalilin sanya Najeriya a wannan jeri ba a lokacin da yake sanar da daukar matakin.

Sai dai tun da farko ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana yadda gwamnatin Najeriyar ta daure ɗaruruan mabiya darikar Shi’a.

Kazalika, ta nuna yadda a wata jihar da Musulmai suka fi yawa aka kama mutanen da suka ki yin azumin watan Ramadana.

Sauran kasashen da Amurka ta sanya cikin jerin masu dakile ‘yancin gudanar da addini su ne China da Iran da Pakistan da Myanmar da Koriya ta Arewa da Saudiyya.

Kasashen da ke cikin wannan jeri za su iya fuskantar takunkumi daga Amurka idan suka gaza inganta tsarinsu na tabbatar da ‘yancin gudanar da addini.

Waiwaye

Zakzaky
Bayanan hoto,Sheikh El-zakzaky na tsare a hannun gwamnati tun 2015

A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta kama shugaban mazahabar Shi’a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky, a lokacin wani samamen soji da ya yi sanadiyyar kashe mabiyansa fiye da 300 a birnin Zaria, a cewar kungiyar Amnesty International.

Sojoji sun zarge su da tare hanya da kuma yunkurin kashe shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.

Mabiya Shi’a sun sha musanta zargin, kuma kotu ta wanke da dama daga cikin mabiya kungiyar da aka gurfanar a gaban kuliya.

Sai dai har yanzu gwamnatin kasar na tsare da Sheikh El-zakzaky duk da umarnin da kotuna daban-daban suka bayar na sakinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Sojojin Najeriya ‘sun kashe ‘yan fashi 48, sun ƙwato mutum 18’

Sojojin Najeriya 'sun kashe 'yan fashi 48, sun ƙwato mutum 18' Dakarun sojan Najeriya sun kashe 'yan fashin daji aƙalla 48 a Jihar Zamfara da...

‘Yan Bindiga sun tilastama wani mawaki da yayi masu waka sana su sako mashi diyar sa

"Yan Bindigar da suka Shiga Garin Shadadi ta Jihar Neja a satin da ya gabata, sun yi garkuwa da Diyar wani Mawaqi kuma sun...

An kubutar da ‘mutum 30 cikin 40’ da ‘yan bindiga suka sace suna Tahajjud a Jibia

An kubutar da 'mutum 30 cikin 40' da 'yan bindiga suka sace suna Tahajjud a Jibia An sace mutanen ne lokacin da suke gabatar da...

Yan bindiga sun sace masu sallar dare sama da mutum 40 a cikin garin Jibia

Yan bindiga sun sace masu sallar dare sama da mutum 40 a cikin garin Jibia Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia Wata majiya ta tabbatar mana da cewa:...
%d bloggers like this: