‘Yan Sanda Sun Cafke Dan Shekara 70 Da Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 11 Fyade A Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan’yan sanda Alhaji Sanusi Buba sun yi nasarar kama wani tsoho, Danladi Habibu, dan shekara saba’in da haihuwa dake zaune a Unguwar Hayin Asibiti a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina, bisa zargin yin lalata da wata karamar yarinya yar shekara goma sha daya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyana haka a lokacin da yake baje-kolin masu laifin daban-daban da rundunar ta kama a helkwatar rundunar da ke Katsina.

Gambo Isa ya ce a ranar 08/3/2021, wani Malam Mamman ya shigar da koken cewa yana zargin Danladi Habibu da yi wa diyarsa ‘yar shekara sha daya fyade a wani gini da ba’a Kammala ba. Ana ci gaba da bincike da zaran an kammala za’a mika shi gaban kuliya domin yi masa hukunci.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Malam Danladi Habibu ya amsa laifinsa, inda ya ce tabbas na aikata wannan lafi da ake zargina da shi kuma ina nadamar aikata shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here