Yan sanda na tarwatsa masu zanga-zangar kafa ƙasar Yarabawa a Legas

Legas

‘Yan sanda a Jihar Legas sun yi amfani da ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar neman kafa ƙasar Yarabawa.

Ana gudanar da zanga-zangar ce a Ojota, inda masu macin suka taru ɗauke da kwalaye masu rubutun goyon bayan ɓallewa daga Najeriya.

A ranar Alhamis ne hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce jami’anta sun kai sumame gidan jagoran zanga-zangar mai suna Sunday Adeniyi Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho da ke garin Ibadan na Jihar Oyo.

Hukumar ta ce ta tura jami’an nata ne sakamakon samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya tara makamai a gidan, inda ta ce ta kashe uku cikin mutanensa masu ɗauke da bindiga tare da kama wasu da kuma makamai da ta samu a gidan.

Sai dai duk da umarnin haramta zanga-zangar da ‘yan sanda suka bayar, mutanen sun fito a yau Asabar domin bayyana ƙudirinsu.

Social embed from facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here