Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta dauka ba a yayin yakin neman zaɓa kafin cikar wa’adinsa.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin sakonsa na Kirsimeti ga ’yan Najeriya, inda ya ce,”Ina taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya, domin gudanar da bikin a wannan shekarar”.

BBC ta rawaito cewa a cikin saƙon, shugaban ya roƙi ƴan Najeriya su yi rigakafin korona, domin rage bazuwar annobar.

Ya kuma taɓo batun tsaro inda ya ce,”Duk da nasarorin da jami’an tsaro su ka samu, amma har yanzu akwai ƙalubale”.

“Ina kira ga ƴan Najeriya da su yi imani da mu da kuma ɗaukar abubuwan da ke faruwa a matsayin wani lokaci da kuma zai wuce, kamar sauran yanayi marar daɗi a tarihin ƙasar.”

Wannan gwamnatin ba za ta yi watsi da alƙawullan da ta yi wa ƴan Najeriya ba,” in ji shugaban”. Inji Buhari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here