Yan majalisar wakilai sun umarci Buhari ya gurfana a gabansu

Yan majalisar wakilai sun umarci Buhari ya gurfana a gabansu

Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi mata bayani kan matsalar tsaron da ta addabi kasar.

Majalisar ta bayyana haka ne a zaman da ta yi ranar Talata.

‘Yan majalisar sun yi kira ga shugaban kasar ya sake fasalin harkokin tsaron Najeriya.

Sun bukace shi ya gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa manoma 43 a Zabarmari a karshen makon jiya, lamarin da ya tayar da hankalin ‘yan kasar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here