Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nemi shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da yayi murabus daga mukaminsa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mambobin kungiyar masu ruwa da tsakin, a cikin wata sanarwar da shugabanta, Kingsley Chinda (PDP, Ribas) da Mataimakinsa, Chukwuka Onyema (PDP, Enugu) suka sa hannu, sun yi wannan kiran ne bayan wata ganawa da suka yi a ranar Asabar.

Sun dora alhakin matsalolin da ke faruwa a jam’iyyar a kan “halayar jagoranci” na Mista Secondus.

‘Yan majalisar na PDP sun kuma zargi Mista Secondus da rashin tafiya tare da ‘yan jam’iyyar, inda suka kara da cewa idan aka ba shi damar ci gaba da mulki a cikin watanni uku masu zuwa, jam’iyyar za ta shiga cikin hadari.

Sun nemi Kwamitin Amintattu (BOT) na jam’iyyar da kungiyar Gwamnonin PDP da su fara sake fasalin jam’iyyar, The News ta ruwaito.

Wa’adin Mista Secondus da sauran membobin Kwamitin Aiki na jam’iyyar na Kasa (NWC) zai kare a watan Disamba bayan an zabe shi a wa’adin shekaru hudu a watan Disamba 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here