A karon farko wasu gamayyar yan kasuwa masu zuba jari a Nijeriya sun buɗe makekiyar maƙabartar da za’a ke biyan kuɗi masu yawa domin rufe gawar Musulmi da Kirista a jihar Ekiti

Gwamnan Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ne ya ƙaddamar da buɗe maƙabarta ta ‘yan kasuwa, wadda sai an biya maƙudan kuɗaɗe kafin a rufe gawa ciki.

Da ya ke jawabi wurin buɗe maƙabartar, Fayemi wanda Kwamishinar Muhalli ta Jihar Ekiti, Iyabo Fokunle, ya ce maƙabartar za ta iya ɗaukar gawarwaki 260,000.

Ya ƙara da cewa maƙabartar wani shiri ne na haɗin guiwa tsakanin Gwamnatin Ekiti da ‘yan kasuwa masu zuba jari.

Fayemi ya ce gina maƙabartar wani ƙoƙari ne daga gwamnatin sa na bunƙasa kasuwanci da zuba jari da aka bijiro da shi a jihar.

Ya ƙara da cewa duk da akwai hannun gwamnatin jiha a harkar kasuwancin, ‘yan kasuwa masu zaman kan su ne za su tafiyar da maƙabartar.

“Buɗe wannan makaranta zai magance barazanar gurɓata muhalli sanadiyyar rufe gawarwaki a gida da wasu ke yi.” Inji Fayemi.

A ƙarshe ya yi kira ga masu zuba jari a cikin kasuwancin su ƙoƙarta su faɗaɗa harkar a cikin ƙananan hukumomi 16 na Jihar Ekiti.

Ya kuma roƙi ‘yan asalin jihar Ekiti mazauna wasu garuruwa cewa idan iyayen su ko ‘yan’uwan su sun mutu, to ɗauko gawar daga can su kawo su rufe a Ekiti, domin a bunƙasa kasuwanci a jihar,

Daya daga cikin daraktocin kamfanin, wanda kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti ne, Abiodun Aluko, ya ce an buɗe bangaren Musulmai daban da na Kiristoci.

Daraktar yace nan gaba kadan za suyi tunanin Bunƙasa kasuwancin su zuwa wasu jihohin a Nijeriya.

Ko yaya kuka kalli wannan al’amarin…?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here