Kaduna

‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kashe aƙalla mutum bakawai a yankunan Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce jami’an tsaro ne suka shaida wa gwamnati faruwar lamarin.

A cewarsa, ‘yan fashi sun harbe mutum huɗu a wajen garin Tsohon Gayan da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.

Kazalika, an kashe wasu mutum biyu da aka bayyana da suna Solomon Bamaiyi da Francis Moses a Kakau, sannan aka kashe wani da ba a bayyana sunansa ba a Kachia.

Ya ƙara da cewa wani mai suna Danjuma Alhaji mazaunin Tsohon Farakwai na Ƙaramar Hukumar Igabi ya rasa ransa a hannun ‘yan fashin a garin Galadima na Ƙaramar Hukumar Giwa.

Kaduna

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here