Home Sashen Hausa Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas yayin zanga-zangar...

Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas yayin zanga-zangar EndSars’

Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas yayin zanga-zangar EndSars’

IGP Mohammed Adamu

Kwamitin bincike da Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kafa domin bincike kan ɓarnar da aka yi wa rundunar ‘yan sandan Najeriya a zanga-zangar EndSars ya ce an sace bindigar Ak-47 kusan 100, a cewar jaridar Punch.

Shugaban kwamitin mai mamba 10, CP Yaro Abutu, ya shaida wa jaridar a yau Asabar cewa baya ga bindigogin, an kuma saci harsashi guda 2,600 yayin tashin hankalin da ya ɓarke sakamakon zanga-zangar.

Ya ƙara da cewa an kai hari tare da lalata wuraren ‘yan sanda guda 37 a jihar. Kazalika, an lalata abin hawansu guda 367, ciki har da motar silke 10 da kuma ƙanana da ƙirar Hilux na fita fatro.

Shugaban kwamitin ya ce suna kuma tattara asarar da ‘yan sandan suka yi a ƙasa baki ɗaya.

Jaridar ta Punch ta ce kwamitin zai miƙa rahotonsa ga IGP Mohammed Adamu nan da mako uku.

Abutu ya koka cewa “abin takaici ne yadda aka aikata ta’asar a ƙarshen shekara, lokacin da aka fi aikata laifuka a faɗin Najeriya”.

“Muna duba abubuwan da suka faru a jiha 17 da aka ƙona ofisoshi da kuma kisan ‘yan sanda. Tun da Legas ce cibiyar zanga-zangar, shi ne muka yanke shawarar fara zuwa nan.

“Ofishin ‘yan sanda 37 aka kai wa hari a Legas kuma an gurgunta kusan kashi 30 cikin 100 na ayyukan ‘yan sandan a jihar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Meat, Tomatoes And Onions Prices Triple As Food Scarcity Looms In Awka

Meat, Tomatoes And Onions Prices Triple As Food Scarcity Looms In Awka By Emmanuel Okonkwo (ABS Reporter) Residents and fresh food dealers in Awka and its...

We brought in Fulani from Mali, Sierra Leone, Senegal, others to win 2015 election, after election, they refused to leave — Kawu Baraje

We brought in Fulani from Mali, Sierra Leone, Senegal, others to win 2015 election, after election, they refused to leave — Kawu Baraje Abubakar Kawu...

THE WHISTLER INVESTIGATION: Banditry In Nigeria: How Security Agencies Aid Illegal Arms Supply (Part 1)

THE WHISTLER INVESTIGATION: Banditry In Nigeria: How Security Agencies Aid Illegal Arms Supply (Part 1) By Tajudeen Suleiman On Mar 3, 2021 Shehu-Rekep-deputy-of-an-armed-group-of-bandits-in-Nigerias-northwestern-Zamfara-state.j Shehu Rekep, deputy of...

‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Uku Da Rana Tsaka A Katsina

'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Uku Da Rana Tsaka A Katsina Da misalin karfe ukku na ranar yau Talata, 'Yan bindiga dauke da bindigogi sun...
%d bloggers like this: