Advert
Home Sashen Hausa 'Yan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a Neja

‘Yan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a Neja

‘Yan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a Neja

Rahotanni na cewa mayakan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a jihar Neja, inda suke bai wa mazauna kauyuka kudi tare da sanya su cikin jerin manyan mayakansu.

Shaidu sun ce ‘yan tada kayar bayan galibinsu dauke da manyan bindigogi sun bulla a wasu kauyukan da ke karamar hukumar Shiroro inda suke yiwa mutane wa’azi, al’amarin da ya jefa jama’a cikin fargaba da tashin hankali.

Bayanan da BBC ta tattaro daga wasu yankuna na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja na cewa, ‘yan Boko Haram din sun karbe garuruwa masu dumbin yawa.

Wani shaida da ya gudu zuwa birnin Minna daga garin Kurebe saboda fargaba, ya shaida mana ta waya cewa, ‘yan Boko Haram suna tara mutane suna yi musu wa’azi.

Baya ga Kurebe, ‘yan Boko Haram din sun kuma bulla a makwaftan garuruwa ciki har da Mashekari da Lukafe da Kusaka da Sabon Gida da kuma Kwaki Chukuba.

Wani mutumin yankin yace har sun fara yiwa mutane hukunci.

BBC ta yi kokarin tuntubar kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris, amma hakata ba ta cimma ruwa ba.

Sai dai rahotan da kamfanin dillancin labarai na Reuter ya yi, ya ambato kwamishinan yana tabbatar da bullar mayakan na Boko Haram a wasu yankuna na karamar Hukumar Shiroro.

Haka kuma, Alhaji Sani ya fadawa Reuters din cewa gwamnatin jihar da kuma jami’an tsaro sun dukufa don dakile bazuwar ‘yan Boko Haram din zuwa wasu yankuna.

A baya-bayan dai kusan ‘yan Boko Haram dubu takwas ne suka miƙa wuya ga hukumomin Najeriya.

Sai dai bullar mayakan ‘yan tada-kayar-bayan a jihar Neja da ke kusa da babban birnin Najeriya Abuja, wani al’amari ne da ke sake fito da bukatar yin hubbasa don kakkebe duk wata barazana da birnin ka iya fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: