‘YAN BINDIGA SUNYI MA SOJOJI KWANTON ƁAUNA

Daga Misbahu Batsari

@Jaridar taskar labarai
Da ranar yau alhamis 04/03/021 wasu’ mahara dauke da muggan makamai suka yi ma sojoji kwanton bauna a kauyen Marina dake cikin yankin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina inda ake zargin sun kashe wasu sojoji cikin ana tsammanin har da mai kula da yankin wagini.
Majiyarmu ta ce wasu sojan sun tsira da raunuka .ance sojojin sun dawo daga wani aiki ne cikin dazuzzukan yankin, sun samo nasara sosai amma akan hanyar su ta dawowa sansanin su dake wagini dai dai kauyen marina maharan sukayi masu kwantar bauna
Mutanen kauyukan sun tabbatar mana da labarin harin amma bamu da tabbacin barnar da akayi tsakanin sojojin da maharan.
Mun aika sakon kar ta kwana ga kakakin soja bamu samu amsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here