Misbahu Ahmad batsari
@ jaridar taskar labarai
Da safiyar yau wakilin jaridun taskar labarai ya je garin tsauwa don ganin abin da ya faru.inda ya samo hotuna da cikakken bayanin abin da ya faru. Ga rahoton shi
Da yammacin ranar litanin 05-07-2021 wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Tsauwa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Sun kai harin ne da misalin karfe 05:45pm inda suka rika bin mutane kan babura suna harbewa.
sannan kuma sun kone kauyen baki daya sai abinda baa rasa ba, sun sace shanu da kananan dabbobi masu yawan gaske.
A zantawar mu da mutanen kauyen sun bayyana mana cewa lokacin da abin ya faru sun sanar wa jami’an tsaro amma dai sunci karensu ba babbaka ba tare da samun wata tirjiya ba.
Bayan sun fita garin sun nufi kauyen ‘Yar Lumo inda suka kwana suna kida (DJ) suna harba bindigu sama suna murnar samun nasara da sukayi a Tsauwa.
An tabbatar da cewa sun kashe mutane goma sha tara sai kuma wasu da baa gansu ba. babu tabbacin suna raye ko kuma akasin haka.
Amma wani dan garin ya Kira wayar dan uwansa sai yaji tana hannun ‘yan bindigar, inda sukace masa kun kashe mana mutum biyu, mu Kuma mun kashe maku linkin abinda kuka kashe mana.
Ga jerin sunayen mutum goma sha takwas da muka samu cikin wadan da barayin daji suka kashe a Tsauwa ciki hadda na’ibin limamin garin;
1.Mallam Bala (Rabe).
2.Abdulmudallib.
3.Sani Lawal (Atti).
4.Suleiman Ashiru.
5.Ashiru Lawal.
6.Mannir Sanusu.
7.Husamatu Kabir.
8.Mansir Ayyau.
9.Shafii Ayyau.
10.Alhaji Salisu.
11.Abdulaziz Iliya.
12.Umar Dan Shehu.
13.Tukur Wada.
14.Abubakar Mande.
15.Malam Bawo.
16.Abubakar Abdulmalik.
17.Iliya Abdulmummuni.
18.Tukur Haruna.

Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here