‘YAN BINDIGA SUN YI DAUKI BA DADI TSAKANIN SU.

Musbahu batsari

@ jaridar taskar labarai

Da misalin karfe 6:00ns ranar Juma’ar da ta gabata ne, wani ayarin ‘yan bindiga masu tarin yawa suka gwabza fada a garin Illela da ke cikin yankin Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina.

Wani da ya nemi mu sakaya sunansa, ya bayyana mana cewa sun kwashe tsawon awa bakwai suna gwabzawa tun 6:00ns, har zuwa 1:00nr.

Majiyar ta bayyana cewa dabar Dan-Karami da Abu Radde ne suka kawo wa Sarki na Illela harin ramuwar gayya.

Shi Sarkin, wani dan bindiga ne da aka ce ya tuba ya daina sata, amma ya koma fada da ‘yan bindigar da ba su karbi sasanci ba, dalili ke nan da ya sa mafi yawansu suke gaba da shi.

Wani ganau ya bayyana mana cewa, ana gama Sallar Asuba ke nan kawai sai ya ji ana cewa kowa ya ruga ga barayi nan. Kafin ka ce kobo, kawai ya ji amon bindugogi na tashi ta ko’ina, jama’a suka rude, kowa yana neman inda zai buya.

Haka dai suka bi gidaje da shaguna suna ballewa suna yin watsi da kayan mutane.

Wani ayarin kuma ya auka kauyen Dagwarwa, inda suka sato dukiya mai yawa, ciki har da tsabar milyoyin kudi na mutanen kauyen da suka sai da dankali.

Haka kuma an yi ta fafatawa da su da yaran Sarki a Illela, amma shi Sarki ya samu agaji daga wani kanensa da ake kira Manin Turuwa, wanda shi ma hatsabibi ne da aka ce ya fi Sarkin zafi, kuma yana da yara (Kwamandoji Daji) hudu da ke karkashinsa wato; Marke, Baushi, Dan Kurma da Yellow.

Dukkansu suna da yaran da ke karkashinsu, kuma sune suka tunkari ayarin ‘yan bindiga aka yi ta dauki ba dadi har ta kai sun kashe matar Manin Turuwa, kuma suka sace daya suka tafi da ita, amma daga bisani sun kwato ta.

Wata majiya ta ce dalilin kai harin shi ne kwanakin baya sun zo sata yankinsa sun sace shanu, ciki har da na Sarkin, amma sai ya kwanta masu ya bude masu wuta. Sannan ya taba kama yan Dan Karami Audu Dan-da ya damka shi ga jami’an tsaro.

Sannan ya jagoranci wani ayari na yaransa suka kai masu hari, har suka gudu suka bar bindigunsu, ciki har da wata babbar bindiga da aka ce suna alfahari da ita. Dalili ke nan da ya sa suka yi masa waya suka ce za su zo a yi fada, haka kuwa aka yi.

Sun tafka fada, kuma an yi asarar rayuka da dama, ciki har da Sarkin Fawan Illela, wanda aka ce sun same shi da bindigar toka.

Har ya zuwa hada wannan rahoton ba mu samu cikakkun alkaluman adadin rayukan da suka salwanta ba daga bangarorin biyu.

Daga bisani an ce Sarki ya tara mutanen Illela ya ba su hakuri. Ya ce ya san saboda shi aka kawo wannan hari, amma su yi hakuri in Allah ya yarda an gama sata a yankunansu. Ya kara da cewa duk inda aka ga barayi a yi masa waya, zai je ya tunkare su, mai rabon ganin badi ya gani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here