Yan bindiga sun sako ɗaliban Bethel Baptist 28 a jihar Kaduna

 

‘Yan bindiga a yau Lahadi 25 ga Yuli, 2021 sun sako ɗaliban makarantar Bethel Baptist su 28 da suka sace a karamar hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an saki daliban ne akan titin Kaduna zuwa Kachia da ke Karamar Hukumar ta Chikun.

Gabanin sakinsu, an samu yara biyu da aka sace tare da su sun tsere daga hannun ‘yan bindigar yayin da suka saki yaro ɗaya saboda matsalar rashin lafiya.

‘Yan bindigar da suka sace yaran a ranar 5 ga watan Yuli sun nemi a basu naira dubu dari biyar kan ko wanne dalibi guda.

Rahotanni na cewa yara 121 ne aka sace baki daya.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, ya tabbatarwa da BBC cewa har yanzu akwai kimanin ɗalibai 80 da ‘yan bindigar ke ci gaba da tsare wa, sai dai kuma bai bayyana cewa ko an biya kudin fansa ba ko ba a biya ba.

A gefe guda kuma ana sa ran yaran da aka saki za su sake haɗuwa da iyayensu da ‘yan uwansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here