Yan bindiga sun sace masu sallar dare sama da mutum 40 a cikin garin Jibia

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa: jiya lahadi da misalin karfe 2:00 na dare, ‘yan bindiga suka shiga unguwar Abbatuwa (Kwata) a cikin garin Jibia dake karamar hukumar Jibia ta jihar katsina, inda suka dira a wani masallachi yayin da ake sallar “Tahajjud” suka yi garkuwa da sama da mutum 40 maza da mata.

Kamar yadda wani mazaunin unguwar da abin yafaru , ya ce har yan bindigar suka tafi da masallatan, ba su sami dauki daga jami’an tsaro ba, a lokacin da abin ya gudana da wajen karfe biyun daren safiyar yau Litinin.

Unguwar da lamarin ya afku ta Kwata na can cikin karshen garin Jibia, karamar hukumar Jibia jihar Katsina.

Karamar hukumar Jibia na daya daga cikin kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here