‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 30 Da Za Su Je Maulidin Sokoto A Jihar Katsina

A kalla matafiya talatin ne, ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a tsakanin hanyar Kankara zuwa Sheme a jihar Katsina.

Majiyar Blueink News Hausa ta ce matafiyan sun taho ne daga jihar Kano da motocin bas bas guda biyu akan hanyar su ta zuwa maulidin shekara-shekara a garin Sokoto a daren jiya Alhamis.

Majiyarmu ta ce farko ‘yan bindigar sun Sace mutane hamsin, amma ganin damar su suka sako ashirin daga cikin su.

Har zuwa aiko da wannan rohotan Blueink News Hausa ba ta da masaniyar ko ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ko ba su tuntube su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here